Jakadan Najeriya a ƙasar Sudan, Ambasada Safiu Olaniyan, ya ce, ofishin jakandancin na jiran sahalewar gwamnatin ƙasar Masar da ta Najeriya kafin wucewar manyan motocin da suka ƙwashe ‘yan ƙasar daga Sudan, ta kan iyakar ƙasar Masar ɗin.
A wani saƙon murya da ya aike wa hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, mista Olaniyan ya ce abin da ake buƙata ga waɗanda ke kan iyakar Sudan da Masar shi ne sahalewar hukumomi, kuma duk abin da ya kamata a yi game da hakan an yi shi.
Ya ƙara da cewa, ba ofishin jakandancin ba ne ke da alhakin samar da motocin.
Ya ce, ofishin na bin umarnin ma’aikatar jin-ƙai da ta bayar da agajin gaggawa NEMA.
Jakadan Najeriya ya kuma tabbatar wa iyaye da ɗalibai cewa jami’an ofishin jakandancin a birnin na Khartoum tare da ‘yan ƙasar a cikin wannan mawuyacin hali na yaƙi da ake ciki.
Mista Olaniyan ya kuma yi kira ga waɗanda za a kwason da su guji far wa jami’an ofishin jakadancin, kamar yadda tun da farko aka yaɗa jita-jita, yana mai cewa babu jami’in ofishin jakadancin da zai fice daga Sudan har sai an tabbatar ‘yan kwashe duka ‘yan ƙasa.