Gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya bayyana burukan sa da zai cimma ga mata a kasar nan, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
Gabanin babban zaben, gwamnan a hukumance ya ayyana burin sa na gaje kujerar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bayan zaben shekara mai zuwa a ranar Laraba a wani taron da ya gudana a Abuja.
Zai tsaya takarar tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), tare da wasu jiga-jigan jam’iyya mai mulki wadanda kuma ke sa ido a kan mafi girman mukami a kasar.
Gwamna Fayemi ya bayyana wasu daga cikin kokarin gwamnatinsa na inganta rayuwar mata da ‘yan mata da kuma inganta shigar mata a jihar Ekiti, inda ya ce, zai yi irin wannan abin kuma ma idan ya ci zaben shugaban kasa.