Guda daga cikin ma’aikacin gwamnatin jihar Sokoto, Ladan Ibrahim. na ɗaya daga cikin mutum 45 da aka damƙe kan zargin taimakawa Boko Haram da kuɗaɗe.
Sai dai iyalan Malam Ibrahim sun bayyana halin da suka tsinci kan su, tun bayan kama jigon da yake ɗaukar nauyin su baki ɗaya, a cewar ta bakin amaryarsa, Habiba Ladan Ibrahim, ta ce abin da za su ci a rana gagarar su yake, balle a yi maganar lafiya da makarantar yara.
Ladan Ibrahim wanda aka kama da zargin hannu a rura wutar ta’addanci wajen tallafawa da kuɗi.
A cewar jaridar Daily Trust, iyalan nasa sun ce sun shiga halin ƙaƙanikayi tun bayan kama shi. A cewarsu tun bayan gayyatar da aka yi masa a ka tsare shi, rayuwarsu ta canza, domin shi kaɗai ke ɗaukar nauyin kula da su da kuma yan uwansa.