Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Abuja da ‘yan bindiga suka saki ranar Litinin ya ce ‘yan uwansu ne suka gana da masu garkuwa da su don kuɓutar da su.
Hassan Usman wanda aka gani a bidiyon da ‘yan bindigar suka fitar ranar Lahadi yana neman ɗauki daga gwamnatocin ƙasashen waje, na cikin mutum uku da aka sako a ranar Litinin.
Ya ce tun ranar Juma’a ‘yan uwan nasa suka yi yunƙurin shiga daji wajen masu garkuwa da su amma sai jami’an tsaro suka hana su. A cewar BBC.
“Sai kuma a jiya [Lahadi] suka sake komawa kuma Allah ya kuɓutar da mu cikin aminci,” in ji shi. Sai dai ya ce ba zai iya bayyanawa ba game da ko an biya kuɗin fansa kafin sakin nasu.
Hassan ya tabbatar da cewa mutanen da suka rage a dajin sun kai aƙalla 40, yana mai cewa su 64 aka kwasa daga jirgin a ranar 28 ga watan Maris da ya gabata – lokacin da suke kan hanyar zuwa Kaduna daga birnin tarayya Abuja.