Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar, wa’adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi kamar yadda ya yi alƙawari.
Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya ce ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln wa’adi ɗaya ya yi na shekara huɗu, “sannan John F. Kennedy bai ma ƙarasa wa’adi ɗaya ba, amma ana cigaba da tunawa da su a matsayin shugabanni masu adalci.”
Ya ce ko a Afirka, Nelson Mandela ya zama abin koyi a duniya wajen shugabanci na adalci, “amma wa’adi ɗaya kawai ya yi.”
“Ba daɗewa a ofis ba ne ke alamta nasara, irin ayyukan da shugaba ya yi ne za a riƙa tunawa. Saboda haka ne nake sake nanata alƙawarin da na yi cewa wa’adi ɗaya na shekara huɗu kawai zan yi idan na zama shugaban Najeriya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ya san ƴan Najeriya ba su cika yarda da maganar ƴan siyasa ba, “amma duk da haka akwai masu cika alƙawari.”
“Na ga wani yana rubuta cewa ko da me zan rantse ba zai yarda cewa wa’adi ɗaya zan yi ba, wani kuma ya ce duk wanda ya ce wa’adi ɗaya zai yi ya je asibitin ƙwaƙwalwa.”
Obi ya ce ya fahimci abin da suke nufi, amma a cewarsa, yana da tarihi mai kyau wajen cika alƙawari tun daga lokacin da ya fara siyasa a Anambra, inda ya ce wata 48 sun isa duk wani shugaba da ya shirya mulki ya yi abin da ya dace.
“Idan na zama shugaban Najeriya a wa’adi ɗaya zan magance matsalar tsaro, zan yaƙi da talauci in inganta aikin gwamnati, sannan zan fifita ɓangaren ilimi da kiwon lafiya, sannan in yaƙi cin hanci da rashawa. Sannan uwa-uba zan inganta ɓangaren noma ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha domin Najeriya ta zama ƙasa mai ciyar da kanta da wasu ƙasashen.”