Hukumar ƙwallon ƙafa ta Italiya (FIGC) ta dakatar ɗan wasan tsakiyar Newcastle da Italiya Sandro Tonali na tsawon wata goma saboda saɓa ka’idojin caca.
Ɗan wasan mai shekaru 23 ba zai sake buga wasa ba har sai watan Agustan baɗi kuma ba zai buga gasar Euro 2024 a bazara mai zuwa ba idan Italiya ta sami cancantar zuwa gasar.
Tonali ya koma Newcastle ne daga AC Milan a watan Yuli kan fam miliyan 55.
A farkon wannan watan aka dakatar da ɗan wasan tsakiya na Juventus, Nicolo Fagioli na wata bakwai tare da cin sa tarar Yuro 12,500 , saboda laifin keta dokokin caca.
An tilasta wa Tonali da ɗan wasan tsakiya Nicolo Zaniolo, wanda ke zaman aro a Aston Villa daga Galatasaray barin sansanin atisayen Italiya a ranar 12 ga watan Oktoba bayan da masu gabatar da ƙara na Italiya suka shaida musu cewa suna da hannu a binciken da ake gudanarwa kan harkokin caca.
Tonali ya buga wasanni 12 a karkashin koci Eddie Howe tun lokacin da ya zama ɗan wasa mafi tsada na biyu da Newcastle ta taɓa siya.


