Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta karɓi sabbin allurai 3,002,400 na allurar rigakafin Covid-19 guda ɗaya na Johnson & Johnson wanda gwamnatin Italiya ta bayar.
Da yake karbar allurar a madadin gwamnatin tarayya a Abuja, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA), Dr Faisal Shuaib, ya ce, za a tura allurar yadda ya kamata a yaki da cutar.
A cewarsa, “Ya zuwa yau 11 ga Afrilu, 2022, mun yi wa mutane 13, 588, 718 allurar riga-kafi.
Ya ce, mutane 23,012,700 ne suka dauki kashi na farko na rigakafin; wanda ke wakiltar kashi 18 cikin ɗari na jimlar yawan mutanen da suka cancanta.
Ya ce: “Na gode da kasancewa tare da mu don karba a madadin gwamnatin tarayya alluran rigakafin Johnson da Johnson Covid-19 miliyan uku da dubu 2 da dari hudu da gwamnatin Italiya ta bayar.
“Ina so in gode wa gwamnatin Italiya, saboda wannan gudummawar da ta yi daidai da kiran da duniya ta yi na samun daidaitattun allurar rigakafin Covid-19. Hakan kuma na nuni ne da irin gaskiya da jajircewar gwamnatin Italiya da tawagar kasashen Turai kan kokarin da duniya ke yi na dakile wannan annoba, domin al’ummar duniya su koma hanyar rayuwa ta al’ada.
A nasa jawabin, jakadan Italiya a Najeriya, Stefano De Leo, ya bayyana cewa, Italiya ta ci gaba da jajircewa tare da sauran mambobin Tarayyar Turai, don tallafa wa Najeriya bukatar allurar rigakafin, da nufin taimakawa wajen fadada yaduwar allurar rigakafi a duniya.