Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish a yammacin Afrika, ISWAP, sun kashe wani kwamandan Boko Haram mai kula da yankunan Sambisa da Gwoza, Ali Gana Alhaji Ali, a tsaunin Gwoza, a karamar hukumar Gwoza a jihar Borno.
Rahotanni sun ce an kashe Ali daya daga cikin jagororin ‘yan ta’adda mafi muni a yankin Arewa maso Gabas a ranar Lahadin da ta gabata, a lokacin da mayakan ISWAP suka yi masa kwanton bauna.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa Aminiya cewa Ali ya kashe mutane da dama a Sambisa da wasu sassan jihar Borno, kafin rasuwarsa a ranar Lahadi.
“Shi ne mataimakin marigayi Ali Ngulde, kuma baya ga Shekau, babu wanda ya kashe mutane kamar sa daga dajin Sambisa da kuma Bayan Dutsen Gwoza.