fidelitybank

ISWAP ta dauki alhakin kisan Mutane 26 a Borno

Date:

Ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kisan mutum 26 a wani hari da ta kai jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Ƙungiyar ta yi wannan iƙirari ne a shafin Telegram.

Lamarin ya faru ne ranar Litinin bayan da wata mota ta taka bam a gefen hanya kusa da iyaka da Kamaru a jihar ta Borno.

Hakan na zuwa ne kimamin mako biyu bayan da wata motar bas ta taka wani abin fashewa da aka binne a yankin, abin da ya janyo mutuwar fasinjoji takwas da kuma raunata wasu 11.

Ƙungiyar Boko Haram da ISWAP sun shafe tsawon shekara 15 suna kai hare-hare da kuma artabu da jami’an tsaron Najeriya a arewa maso gabas.

Sun sha amfani da abubuwan fashewa wajen afkawa fararen hula da kuma jami’an tsaro.

sun news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp