fidelitybank

ISWAP sun kai hari jihar Yobe

Date:

Da sanyin safiyar Asabar ne wasu ‘yan ta’addan da suka fito daga yankin yammacin Afirka ta ISWAP suka kai wani kazamin hari a garin Geidam da ke jihar Yobe, inda suka kashe wani mazaunin garin tare da yin barna mai yawa kamar yadda majiyoyi da dama suka bayyana.

An fara kai harin ne da misalin karfe 3:30 na safe lokacin da maharan suka far wa garin, inda suka rika harbin bama-bamai ba gaira ba dalili tare da tsoratar da mazauna garin.

Majiyoyin leken asiri sun bayyanawa wani kwararre a fannin yaki da ‘yan ta’adda Zagazola Makama cewa maharan sun lalata kadarori tare da kona wasu motoci biyu na jami’an hukumar kwastam ta Najeriya.

An ce mayakan sun lalata kabarin Khalifah Ayiloma da ke unguwar Kolori, inda suka cinnawa kabarin wuta.

Sun kuma kai hari gidan wani mai gadin dare Dahiru Muhammadu mai shekaru 60 da ke kusa da Geidam Polytechnic. Muhammadu ya samu rauni a wuyansa, inda aka garzaya da shi asibitin kwararru na Geidam, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

news today in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp