Majalisar Isra’ila ta yanke shawarar rufe duk wasu ayyukan gidan talabijin na Al Jazeera daga ƙasarta kan dalilin cewa tana barazana ga lamuran tsaronta.
Matakin zai haɗa da rufe ofishin gidajn talabijin ɗin da ke Isra’ila, da kwace kayan aikin yaɗa labaranta, da yanke duk wasu wayoyin tashar daga tauraron ɗan adam ɗinta sannan ta toshe shafin tashar na Intanet.
Manajan tashar ya bayyana matakin a matsayin mai cike da haɗari, inda ya ce tawagar tashar ta ɓangaren shari’a na shirya matakin da za ta ɗauka.
Tun tuni hukumomin Al jazeera suna sukar tashar wadda ke samun goyon bayan Qatar da nuna kin jinin Isra’ila.
Wakilan Al Jazeera na daga cikin ‘yan jarida ƙalilan da ke cikin Gaza suke kawo rahoton yakin da ake yi.