Isra’ila ta yanke shawarar aika wata tawaga zuwa Qatar yau Lahadi domin tattaunawa da Hamas kan shawarar baya-bayan nan ta neman tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin mutanen da ƙungiyar ke tsare da su.
Ofishin Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce shugaban ya amince da gayyatar duk da rashin gamsuwa da sauye-sauyen da Hamas ta nema a yi wa tsarin da masu shiga tsakani daga Qatar da Amurka da Masar suka gabatar.
A raanr Juma’a ne Hamas ta ce ta gabatar da matsayarta ga shawarar tsagita wutar na tsawon wata biyu kuma a shirye take ta shiga tattaunawar.
Sai dai wani jami’in Falasɗinawa ya ce ƙungiyar ta nemi a yi gyare-gyare da ya haɗa da samun tabbacin cewa Isra’ila ba za ta ci gaba da kai farmaki ba ko da ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin ba.