Rundunar sojin Isra’ila ta ce garkuwar tsaron samanta da aka fi sani da Iron Dome, ya dakile wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen kafin ya surare ya fada yankin Eilat da ke kudancin kasar.
Harin na zuwa ne bayan jiragen yakin Isra’ila sunka kai wasu jerin hare-hare a ranar Asabar a tashar ruwan Hodeidah da ke karkashin ikon Houthi a kasar Yemen.
Kafofin watsa labaran gwamnatin Houthi sun ce harin ya shafi wani rumbun adana man fetur, lamarin da ya yi ajalin mutane uku.
Houthi dai ta ce Isra’ilar za ta dandana kudarta.
Tun da farko, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga bangarorin biyu da su maida wukarsu cikin kube. In ji BBC.