Isra’ila ta ce ta kai wasu jerin hare-hare kan wasu wuraren aikin soja a Iran, a matsayin martani ga abin da ta kira ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila da Iran da kawayenta ke yi.
Kakakin sojin Isra’ila Daniel Hagari, ya ce ramakon tamkar wani nauyi ne da ya rataya a kan kasar, biyo bayan harba makami mai linzami kusan dari biyu da Iran ta harba masu a makonni uku da suka wuce.
Kamfanin dillancin labarai na Iqna ya ce an kai hari kan wasu sansanonin soji a yamma da kudu maso yammacin Tehran babban birnin kasar Iran.
Wakilin BBC a birnin Kudus ya ce Isra’ila ta takaita hare-haren na kan wuraren soji kadai kuma ba ta kai hari kan tashoshin nukiliya ko matatun man fetur ba.
An rawaito wani babban jami’in Iran na cewa za su mayar da zazzafan martani a lokacin da ya dace
Kasadar Iran ta kai wa Isra’ila hari bayan yin illa ga ƙawayenta
4 Oktoba 2024
An kuma bayar da rahoton tashin bama-bamai a Damascus babban birnin kasar Syria.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarto jami’an gwamnatin Syria na cewa, naurorin kakkabo makamai daga sama na kakkabo makaman makiya.
An kuma sami rahotannin fashewar wasu abubuwa a Iraki, (a Diyala da Salah Al-Din) kusa da Bagadaza babban birnin kasar.
A birnin Washington fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce babu hannun Amurka a cikin lamarin.
Wani mai magana da yawun fadar ya ce an sanar da mataimakiyar shugabar kasar Kamala Harris wadda ke yakin neman zabe a Texas halin da ake ciki.