Shugaba Biden na Amurka ya fito fili ya yi kira ga Isra’ila a kan ta rinka taka tsantsan, a yayin da sojojin ƙasar ke shirin fara kai hare hare ta kasa a Gaza.
Cikin wata hira da ya yi da kafar yada labaran CBS, Biden ya ce ya yi amanna za a kawar da Hamas, to amma babban kuskure ne ga Isra’ila ta mamaye Gaza.
Kazalika shugaban na Amurka, ya ce, akwai buƙatar a samu hukumar Falasdinawa, da kuma hanyar samar da ƙasar Falasdinawa.
Ya ce yana da yakinin cewa Isra’ila za ta yi aiki ne da doka a yakin da ta ke a Gaza, sannan kuma ya yi amanna cewa mutanen da ke wajen waɗanda ba suji ba su gani ba za su iya samun abinci da ruwan sha da kuma magunguna.


