Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya ce ayyukan Isra’ila “sun wuce iyaka” kuma “za su iya tilasta kowa da kowa ya ɗauki mataki”.
Cikin wani saƙon X – wanda aka sani da Twitter a baya – Raisi ya ƙara da cewa: “Amurka ta nemi kada mu shiga yaƙin amma tana ci gaba da nuna goyon baya ga Isra’ila. Amurkar ta aika saƙonni ga Dakarun Ƙawance ‘yan Gwagwarmaya kuma ta gamu da martani ƙarara a filin yaƙi.”
“Dakarun Ƙawance ‘yan Gwagwarmaya” na nufin ƙawancen ƙungiyoyin da Iran ke mara wa baya a faɗin Gabas ta Tsakiya, wanda Hamas ke ciki.
Hukumomin Amurka sun sha gargaɗin Iran da kada ta shiga yaƙin Isra’ila da Hamas da zimmar hana yaƙin yaɗuwa.
Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon wadda ita ma ke samun taimakon Iran, mayaƙanta na ci gaba da gwabzawa da na Isra’ila a ‘yan makonnin nan.