Ministan harkokin wajen Isra’ila, Eli Cohen, ya ce za a soke takardar izinin zama na Lynn Hastings, jami’ar kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasɗinawa, saboda abin da Cohen ta ce na ƙin yin magana kan Hamas.
Da yake zargin Majalisar Dinkin Duniya da “son kai”, Cohen ta rubuta a cikin wani sakon da ta wallafa a kan shafin sada zumunta na X, in da tace,
“Wacce ba ta la’anci Hamas ba kan mummunan kisan kiyashin da ta yi wa Isra’ilawa 1,200 da sace jarirai da tsofaffi da kuma mummunan ayyukan cin zarafi da zalunci kuma fyade, da yin amfani da mazauna Gaza a matsayin garkuwar ɗan adam, amma kuma ta la’anci Isra’ila, ƙasa mai mulkin demokraɗiyya da ke kare ‘yan ƙasa, ba za ta iya aiki a Majalisar Dinkin Duniya ba kuma ba za ta iya shiga Isra’ila ba!”
Isra’ila ta ci gaba da sukar Majalisar Dinkin Duniya kan martanin da ta mayar kan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Hastings ta kasance mai sukar hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Gaza kuma ta jagoranci kiraye-kirayen kara kai agajin jin kai a Gaza.
A ranar Litinin, wata sanarwa da Hastings ta fitar ta ce: “Sharuɗɗan da ake buƙata don isar da kayan agaji ga al’ummar Gaza ba su wanzu ba, idan har zai yiwu, wani yanayi mai bala’i da munnin gaske na gab da afkuwa, wanda ayyukan jin kai ba za su iya mayar da martani ba.”
Ta ce rashin tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli da rashin abinci mai gina jiki ga mutane “ka’idan za su haifar da annoba da kuma bala’in lafiyar jama’a”.