Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a kudancin Lebanon ta ce wata motar rushe gine-gine ta Isra’ila ta lalata shingen tsaro da kuma katangar daya daga cikin sansanoninta.
Wannan shi ne lamari na baya-bayan nan cikin jerin abubuwan da suka auku bayan kiran da Isra’ila ta yi da a janye dakarun rundunar ta UNIFIL daga Lebanon.
Kakakin rundunar ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIFIL) a Beirut, Andrea Tenenti, ya gaya wa BBC cewa wannan wani harin ne cikin waɗanda suka sha fama da su a cikin makonnin da suka gabata daga rundunar sojin Isra’ila.
Kakakin ya ƙara da cewa wannan lamari ne da ya saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.