Isra’ila ta nemi Rasha ta kare “‘yan ƙasarta da kuma dukkan Yahudawa” bayan wani dandazon wasu mutane sun kutsa filin jirgin sama na Dagestan suna ta ihun ƙin jinin Yahudawa.
Wani bidiyo da aka wallafa a intanet ya nuna yadda mutanen cikin fushi suke shiga sassan filin jirgin da ke Makhachkala a Rasha suna neman matafiyan da suka sauka daga birnin Tel Aviv.
Wasu daga cikin mutanen sun shiga har kan titin tashin jirgin kuma suka zagaye shi.
Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Rasha, Rosaviatsia, ta ce ta shawo kan lamarin daga baya.
An rufe filin jirgin ranar Lahadi da dare. Rosaviatsia ta ce an sake buɗe shi a ranar Litinin, amma ta ce jiragen da suke zuwa daga Isra’ila “za a dinga sauya musu masauki zuwa wasu filayen jirgin na ɗan lokaci.”.
Kamfanin dillancin labarai na Rasha ya ce an kama mutum 60 daga cikin fusatattun mutanen yana mai ambato ma’aikatar harkokin cikin gida.