fidelitybank

Isra’ila ta lalata hanyoyin Hamas na ƙarƙashin ƙasa 130

Date:

Dakarun tsaron Isra’ila sun ce sun lalata hanyoyin ƙarƙashin ƙasa na Hamas 130 tun bayan fara kai farmakin ƙasa a Gaza.

A cikin wata sanarwa da dakarun Isra’ilar suka fitar sun ce “A halin yanzu dakarun yaƙin ƙasar suna aiki don fallasa tare da lalata kayayyakin ‘yan ta’adda na Hamas a Gaza, ciki har da hanyoyin ƙarƙashin ƙasa.”

“Ruwa da kuma ajiyar iskar oxygen da aka gano a cikin hanyoyin na nuni da shirye-shiryen Hamas na tsawaita zama a karkashin kasa.” in ji sanarwar.

A ranar Laraba ne rundunar sojin ta ce ta lalata wata hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Hamas da ke kusa da wata makaranta da Hukumar Agaji ta Falasɗinu ke ɗaukar nauyinta a yankin Beit Hanoun da ke arewacin Gaza.

Rundunar ta kuma wallafa wani bidiyo da ake zargin ya nuna ɓarnar da aka yi a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ke kusa da makarantar.

Isra’ila ta fara kai hare-hare a Gaza bayan harin Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 1,400 tare da yin garkuwa da sama da 200.

Rundunar ta kuma tabbatar da mutuwar wani soja guda wanda ya kai adadin sojojin da aka kashe a harin ta ƙasa zuwa 31.

Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe a Gaza ya karu zuwa 10,569 tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hare-haren ramuwar gayya.

www.punch news.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp