Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce yara 2,360 ne suka mutu a hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai a kudancin Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kungiyar agajin, wacce ta yi magana game da “hare-haren da ba a saba gani ba”, ta ce yara 5,364 sun jikkata.
Tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, sojojin Isra’ila ke kai hare-haren bama-bamai a zirin Gaza tare da shirya kai farmaki ta kasa a yankin da aka rufe.
“Halin da ake ciki a Zirin Gaza wani tabo ne a kan lamirinmu na gamayya. Adadin mace-mace da jikkatar yara na da ban mamaki,” in ji Adele Khodr, darektan UNICEF na yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.
Ya ce yankin na Gaza na fama da matsalar karancin ruwan sha, tare da yin mummunar illa ga kananan yara wadanda ke da kashi 50 cikin 100 na al’ummar kasar.
UNICEF ta bukaci dukkan bangarorin da su amince da tsagaita bude wuta, samar da agajin jin kai da kuma sako duk wadanda aka yi garkuwa da su. (NAN)


