Mai magana da yawun rundunar sojin Hamas ya ce, kimanin ‘yan Isra’ila 50 da mayaƙanta ke garkuwa dasu a Gaza, aka kashe sakamakon hare-harenda Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza, bayan mummunan harin da Hamas ta kai ranar 7 aga watan Oktoba.
Abu Obeida bai yi cikakken ƙarin bayani kan mutanen da aka kashen ba. Haka kuma BBC ba ta iya tabbatar da wannan adadi ko wani bayani da ta fitar ba.
Sojojin Isra’ila sun bayyana sunayen mutum 224 da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.


