Wani harin da Isra’ila ta kai kan wani gini da ke tsakiyar Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon ya kashe aƙalla mutum shida tare da jikkata wasu shida, kamar yadda jami’a Lebanon suka bayyana.
Ta jefa bam ɗin ne a wani bene da ke Bachoura, kusa da majalisar dokokin Lebanon, wanda shi ne hari na farko da Isra’ila ta kai a babban birnin ƙasar.
Haka kuma sun kai hari a Dahieh, wanda shi ne yankin da Hezbollah ta fi ƙarfi. In ji BBC.


