Ministan lafiya na ƙasar Lebanon, Firass Abiad ya ce mutum 558 ne hare-haren Isra’ila suka kashe sannan 1,800 suka jikkata daga ranar Litinin zuwa yanzu.
Da yake magana a wani taron manema labarai, ministan ya shaida wa ƴanjarida cewa mutum 1,835 ne suka jikkata a tashin bama-baman inda ya ce ma’aikatan lafiya na iya ƙoƙarinsu wajen kula da marasa lafiyar.
Abiad ya ƙara d acewa ma’aikatan lafiya huɗu sun mutu a ranar Litinin lokacin da Isra’ila ta antayo hari kan wata motar ɗaukar marasa lafiya.
Dangane kuma da mutum fiye da 500 da aka kashe, ministan ya ce 50 daga ciki ƙananan yara ne.
Bayanai dai sun nuna cewa ranar Litinin ta fuskanci hare-hare mafi muni a Lebanon tun shekarar 1990 lokacin yaƙin basasa.