Ɗaruruwan ƴan Lebanon ne hare-haren Isra’ila ya kashe a cigaba da cigaba da luguden wuta da ƙasar ke yi da Lebanon.
Rahotanni na nuna an kashe kusan mutum 492, sannan an raunata sama da 1,645 a ƙasar Lebanon, kamar yadda Ma’aikatar Lafiyar ƙasar ta bayyana.
Wannan shi ne karon-batta mafi muni tsakanin Isra’ila da Hezbollah tun bayan da suka fara takun-saƙa a shekarar 2006′
Tuni dubban fararen hula suka tsere daga gidajensu domin tsira daga hare-haren a daidai lokacin da Isra’ila ta ce ta kai hari a wuraren Hezbollah guda 1,300.
Tun farko, Firaiministan Isra’ila, Benjamin Natanyahu ya yi kira ga fararen hula a Lebanon da su matsa daga wuraren da Isra’ilar take luguden wuta, sannan sojojin Isra’ila sun riƙa aika saƙonni ta wayar salula ga fararen hular suna nanata saƙon na Natanyahu.
Rahotanni a Lebanon sun nuna cewa Isra’ila na harin wani babban kwamandan Hezbollah mai suna Ali Karaki ne da ke Kudancin Lebanon, amma har yanzu babu tabbacin ko sun kashe shi, duk da cewa Hezbollah ta ce yana ƙalau.
Ita ma dai Hezbollah ta aika da sama da rokoki 200 a arewacin Isra’ila.
A ɗaya gefen kuma, Amurka ta ce za ta aika da ƙarin dakaru zuwa yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce za su yi hakan ne domin hana ta’azzarar yaƙe-yaƙe domin mutane su koma gidajensu lafiya.