Shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa ya zargi Isra’ila da kai munanan hare-hare kan fararen hula da gine-ginen gwamnatin ƙasarsa.
Isra’ila ta ce sojojin Syria sun kai hari kan fararen hula ƴan al’ummar Druze a birnin Sweida.
A jiya Laraba Isra’ilar ta kai hare-hare ta sama kan ma’aikatar tsaro da fadar shugaban ƙasar Syria.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce jami’an diflomasiyyarsa sun kwashe tsawon dare suna aiki domin warware rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Mista Rubio ya ƙara da cewa ”wannan lamari ne mai cike da sarƙaƙiya, da aka daɗe ana yinsa tsakanin ɓangarori daban daban kuma hakan ya janyo matsalar rashin fahimta tsakanin Syria da Isra’ila amma muna fatan nan bada jimawa ba za a shawo kan lamarin”.