Jami’an Hezbollah sun ce, hare-haren Isra’ila ta sama a tsakiyar Lebanon sun kashe jam’in yaɗa labaran ƙungiyar.
Muhammad Afif na ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar ƙalilan da suka rage.
A ranar Litinin da ta wuce ne aka yi wa mista Afif ganin ƙarshe a wani taron manema labarai a wajen kudancin Beirut, inda ƙungiyar take.
Haka kuma sojojin Isra’ilar sun kai hari kan wani wajen sojin Lebanon inda suka kashe soja ɗaya da raunata wasu uku a kudancin ƙasar.
Wannan wata alama ce da ke ƙara nuna cewa babu wani tudun mun tsira a Beirut, saboda an kai wannan harin ne ba tare da wani gargaɗi ba.