Kusan mutum 3,000 ne suka rasa rayukansu a Zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba sakamakon hare-haren Isra’ila, a cewar ma’aikatar lafiya ta Falasɗinu.
Sanarwar da aka wallafa a Facebook ta ƙara da cewa an jikkata wasu mutum 12,500.
Kazalika, an kashe wasu Falasɗinawan 61 a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan (West Bank), wanda Isra’ila ta mamaye da kuma raunata 1,250.


