Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe ƙarin Falasɗinawa 193 tun lokacin da Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza ranar Juma’a.
Ta ce an kuma raunata wasu mutum 652 tun bayan ƙarewar wa’adin tsagaita wuta na kwana bakwai.
A cewar sanarwar da ta fitar, jimillar Falasɗinawan da aka kashe a Gaza sun zarta 15,000 tare da raunata sama da 40,000 – kashi 70 cikin 100 na mutanen mata da ƙananan yara.


