Rundunar sojin Iran ta musamman Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC), ta tabbatar da mutuwar Birgediya Janar Abbas Nilforoushan yayin harin da ya kashe Hassan Nasrallah, shugaban Hezbollah.
Cikin wata sanarwa, ba a yi wata magana kan ɗaukar fansar kisan nasa ba, duk da cewa IRGC ta siffanta harin da “laifukan gwamnatin Yahudawa” a Lebanon.
IRGC ta sha yin alƙawarin rama kisan shugaban Hamas Ismail Haniyeh da aka kashe a Tehran a watan Yuli, wanda aka yi imanin Isra’ila ce ta aikata.
Sanarwar ta ce janar ɗin mai ba da shawara ne na IRGC a Lebanon.


