An samu ƙarin hare-hare ta sama da fashewar bama-bamai a arewacin Gaza cikin dare.
An ba da rahoton sake samun katsewar intanet da amfani da wayar tarho a yankin amma a daren wakilin BBC a Gaza, Rushdi Abualouf ya shaida cewa yana ganin an kai hare-hare ta sama mafi muni tun farkon yaƙin.
Ya ce an kai hare-haren ne kan arewa maso yammacin Gaza, inda aka yi ruwan bama-bamai a sansanin ‘yan gudun hijira na bakin teku wanda aka fi sani da sansanin Shati.
Kuma a cikin sa’a da ta wuce, Isra’ila ta ce jiragen yakinta sun kai hari a wurare 450 a yankin.
Bisa sabon alƙalumman da jami’ai suka fitar, an kashe fiye da mutum 9,700 a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
A Isra’ila, Hamas ta kashe mutane sama da 1,400 tare da yin garkuwa da wasu sama da 200.