Rundunar sojin Isra’ila ta ce, matakan tsaron sararin samaniyarta sun kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harba daga ƙasar Yemen.
Rundunar ta IDF ta ce an harbo makamin kafin ya isa yankin Isra’ila.
Ƴan tawayen Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran sun yi ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki kan Isra’ila a matakin da suka ce nuna goyon baya ne ga Falasɗinawa.