Sojojin Isra’ila sun ce sun kai mamaya ta ƙasa da tsakar dare a Zirin Gaza, a wuraren da Hamas ke iko da su.
Mai magana da yawun sojin Laftanal Kanal Jonathan Concirus ya shaidawa BBC cewa dakarun sun kai harin share fage gabannin kai hari ta kasa da suke shirin yi.
Ya ce sun yi abin da ake kira share fage, inda sojoji suka shiga da daddare kuma suka fito, domin shirya fagen daga, da shirya kan su kan aikin da ke tafe inda ya ce a yanzu dakarun sun koma Isra’ila.
Ya ƙara da cewa sun yi aikin cikin nasara ba tare da wata tangarɗa ba.


