Isra’ila ta ce ta kai hare-hare kan gomman gine-gine da a cikinsu akwai bankunan Al-Qarda al-Hassan (AQAH) – bankin da Isra’ila ta ce yana taimakon Hezbollah.
Akwai sassan bankin guda 34 a cikin Lebanon. Sannan kafofin watsa labarai na ƙasar Lebanon sun ruwaito cewa an kai aƙalla hare-hare guda 16 a sassan bankin a kudancin Beirut.
Tun da farko, rundunar tsaron Isra’ila ta gargaɗi mutanen da suke zaune a sama da yankuna 20 a Lebanon – ciki har da yankuna 14 a babban birnin ƙasar – inda ta ce za ta yi luguden wuta a yankunan.