Ma’aikatar harkokin cikin gidan FalasÉ—inawa ta Hamas a Gaza ta sanar da cewa, a daren jiya Isra’ila ta kai hare-haren bama-bamai ta sama kan gidaje a birnin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran FalasÉ—inawa Wafa ya bayyana cewa, an kashe fararen hula da dama sakamakon hare-haren a birnin Gaza.
Dakarun sojojin Isra’ila ba su bayar da takamaiman bayani kan waÉ—annan hare-hare ta sama ba.
Idan dai ba a manta ba a baya Isra’ila ta kwashe makonni tana gargadin mutane da su fice daga birnin Gaza da arewacin yankin, amma dubbai sun rage.
Ya zuwa ranar Talata, hukumomin yankin sun bayyana cewa har yanzu mutane kusan 600,000 ne ke zaune a Gaza da yankin arewa.”


