Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da hare-hare ta kasa kan Hezbollah a Lebanon.
Sojojin Isra’ila sun ce hare-haren nasu a yanzu sun hada da ta sama da kasa, inda kuma suke amfani da makaman atilare da bama-bamai.
Wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar IDF ta fitar ta ce suna kai farmaki ne kan maboyar Hezbollah a kauyuka da ke kusa da iyakarsu da Lebanon.
Daya daga cikin hare-haren nasu ya fada a sansanin Falasdinawa da ke kusa da Sidon a kudancin Lebanon.
Kafin wannan kuma, hare-hare ta sama da suke kai wa a Beirut na sake kamari bayan sun gargadi mazaunan yankin kudancin birnin su fice.
Mataimakin shugaban Hezbollah Sheikh Qasssem ya jadadda cewa mayakansu a shirye suke domin tunkarar mamayar Isra’ila.


