Ƙungiyar agaji ta Red Cross a ƙasar Lebanon ta ce, an aike da tawagogin motocin ɗaukar marasa lafiya zuwa Sirbine da ke kudancin Lebanon, bayan wani hari ta sama da aka kai a safiyar yau.
Ta ce an ɗan jikkata masu aikin sa-kai a wajen aikin ceto – lokacin da aka kai hari karo na biyu a yankin.
“Ya kamata a kare masu sa-kai na Red Cross a Lebanon a kowane lokaci yayin da suke ƙoƙarin ceto waɗanda suka jikkata,” kamar yadda sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta bayyana. In ji BBC.