Dakarun sojin Isra’ila sun yi ta jefa takardun gargaɗi ga mazauna Khan Younis da ke kudancin Gaza, inda a ciki suke kiransu da su fice daga yankin zuwa kudanci domin samun kariya.
An yi ta yaɗa hotunan takardun gargaɗin a shafukan sada zumunta, waɗanda ke cewa Khan Younis ya zama wuri ”mai hatsarin faɗa”, tare da kiran mutanen yankin gabashin garin da su fice zuwa kusa da Rafah da ke kusa da kan iayakar Masar.
An dai yi ta jefa takardun makamancin wannan gargaɗi a wasu wuraren tun bayan fara yaƙin, a wani mataki da rundunar sojin Isra’ilar ta kira da ”hanyoyin kauce wa cutar da fararen hula a Zirin Gaza”.


