Ministan harkokin wajen Isra’ila, Eli Cohen, ya umarci jami’an diflomasiyyar ƙasarsa da ke Turkiyya su koma gida.
Cikin wani saƙon X da ya wallafa, Mista Cohen ya ce an ɗauki matakin ne bayan abin da ya kira ”kakkausar sanarwa” daga Turkiyya.
A yau ne shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kira hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza da “kisan kiyashi”.