Isra’ila ta kashe wasu ƴan jarida biyar a wani hari da ta kai kan motarsu a yau Alhamis, a ƙofar wani asibiti a Gaza, kamar yadda hukumomin lafiya a Zirin suka bayyana.
Daga cikin ƴanjaridan da aka kashe, akwai wanda yake tsimayin haihuwar matarsa.
Sai dai a ɓangaren rundunar sojin Isra’ila, ta musanta kashe ƴanjaridar, inda ta ce sojojinta sun ce waɗanda suka kashe ƴan ƙungiyar ta’adda ne.