A jiya, ƙungiyar ‘yan tawayen Houthi a ƙasar Yemen – mai nisan mil dari kudu da Isra’ila – ta ce ta kai hari kan Isra’ila har sau uku da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, kuma za su sake kai wasu hare-haren.
Yanzu haka dai rundunar sojin Isra’ila ta ce ta girke jiragen ruwanta na yaƙi a tekun Maliya domin ƙarfafa matakan tsaro a yankin.
Da sanyin safiyar Larabar, rundunar IDF ta ce ta dakile wani hari ta sama daga tekun Bahar Maliya a kudancin birnin Eilat da ke kudancin Isra’ila.