Dakarun sojin Isra’ila sun ce, sun gano gawar mutum uku da aka yi garkuwa da su a Zirin Gaza
A cewar rundunar sojin ƙasar ta IDF, mutanen su ne Shani Louk, da Amit Buskila, da Itzhak Gelerenter.
IDF ta ce an kashe su ne tun ranar 7 ga watan Oktoba kuma aka ɗauki gawar ta su zuwa Gaza.
Kafofin yaɗa labaran Isra’ila sun ruwaito cewa, an gano gawarwakin ne cikin wata hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Hamas.
Mutane aƙalla 1,200 aka kashe lokacin da ‘yan gwagwarmyar Falasɗinawa suka aukawa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba, sannan suka yi garkuwa da aƙalla mutane 252.
A matsayin martani, Isra’ila ta kashe sama da mutane 35,000, kamar yadda ma’ikatar lafiya ta Gaza ta tabbatar.
Sai dai Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana labarin da mai karya zuciya.
Ya na mai cewa, za su dawo da dukkan mutanen su da aka yi garkuwa da su, masu rai da matattu.