Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta gano gawar ”yan ƙasar biyu da aka yi Garkuwa da su a Zirin Gaza.
Wasu mayaƙa ne suka kashe Judi Weinstein Haggai mai shekara 70, wadda ‘yar ƙasar Canada ce kuma, da mijinta Gadi Haggai mai shekara 72 lokacin da suka kai hari a Kibbutz Nir Oz da ke cikin Isra’ila a watan Oktoban 2023, in ji wata sanarwa.
An gano gawarwakin nasu ne a kudancin Khan Younis da ke Gaza da tsakar dare kuma aka mayar da su Isra’ila domin gudanar da bincike.
Har yanzu akwai mutum 56 da ake yin garkuwa da su a Gaza, cikinsu ana tunanin 20 na raye a hannun mayaƙan ƙungiyar Hamas.