Sojojin Isra’ila sun fitar da faifan bidiyo da ke nuna shugaban ƙungiyar Hamas Yahya Sinwar a mintunan karshe kafin halaka shi.
Bidiyon wanda wani jirgin sama mara matuki ya naɗa ya nuna wani mutum zaune da rauni a kan kujera, riƙe da itace a tsakiyar wani rusasshen gini, yayin da ya rufe fuskarsa da tutar Falasɗinu.
Kakakin rundunar sojin Isra’ila Daniel Hagari ya ce an kashe ƙarin wasu mutane biyu a farmakin.
Mista Hagari ya ce dakarunsu za su ci gaba da bibiyar sauran shugabannin ƙungiyar Hamas da nufin kawo karshensu.