Isra’ila ta ce ta soma gwada amfani da sabuwar na’urarta ta kakabo makamai masu linzami.
An yi amfani da na’urar wajen kakabo wasu makamai masu linzami da aka harba mata a tekun Baharum.
Wannan sanarwa na zuwa ne sa’o’i bayan ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon-bayan Iran a Yemen sun sanar da harba shu’uman makamai masu linzami kan Isra’ila.
‘Yan tawayen na Houthi sun kai wa Isra’ila hare-hare babu iyaka tun soma yakin Gaza a watan da ya gabata.