Hanyoyin sadarwa na waya da internet sun fara dawowa a Zirin Gaza bayan Isra’ila ta katse su yayin da take ƙara kai hare-hare a yankin.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce muhimmin abubuwan da ya sa a gaba shi ne rusa Hamas tare da kuɓutar da mutanen da take garkuwa da su.
Yanzu haka Isra’ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza tare da kai farmaki ta ƙasa bayan Mista Netanyahu ya bayyana cewar yaƙin zai ɗauki dogon lokaci.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Hamas a Gaza ta ce akalla mutum 8,000 aka kashe tun bayan kaddamar da hare-hare ta sama a matsayin martani ga kisan da Hamas ta yi wa Isra’ilawa 1,400 mako uku da suka gabata.