Tawagar masu aikin ceto a Isra’ila na ci gaba da neman mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine a birnin Tel Aviv.
An ji ƙarar fashewar manya-manyan abubuwa a wasu biranen Isra’ila ciki har da Tel Aviv da Jerusalem, yayin da Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami cikin dare zuwa Isra’ila.
Hotunan da aka wallafa a Intanet sun nuna yadda gine-gine suka ruguje.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Isra’ila ta ce mutum biyar ne suka mutu sannan wasu sama da casa’in suka jikkata, a hare-haren na cikin dare.
Ƙasashen Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta cikin dare a yayin da aka shiga kwana na huɗu a rikici tsakanin kashen biyu.
Hare-haren na Iran sun kuma shafin birnin Haifa da ke arewacin ƙasar, wanda ya kasance cibiyar babbar tashar jirgin ruwa da matatar matar mai.
Tun da farko Iran ta tabbatar da cewa an kashe shugaban sashen leƙen asiri na rundunar dakarun ƙare juyin juya hali ta ƙasar da mataimakinsa da wani kwamanda a wani harin da Isra’ila ta kai birnin Tehran.
Ma’aikatar lafiyar Iran ta ce aƙalla mutum 224 ne suka mutu tun bayan aka fara kai mata hare-haren.
A nata ɓangare Isra’ila ta ce kawo yanzu an kashe mutum 19, tun bayan fara hare-haren