Ministan tsaron Isra’ila, Isreal Katz ya ce ya umarci dakarunsu da su ƙaddamar da hare-hare a yankin gaɓar yamma da kogin Jordan da aka mamaye, bayan fashewar wasu motocin bas uku da babu kowa a cikinsu a kusa da Tel Aviv.
Babu rahoton jikkata daga fashewar motocin, an kuma samu nasarar lallata ƙarin wasu bama-bamai a cikin wasu motocin daban.
Wakiliyar BBC ta ce kafofin watsa labaran yankin sun ruwaito cewa a cikin bama-baman da ƴansanda suka yi nasarar kwancewa, guda daga ciki an rubuta saƙon ɗaukar fansa kan samamen da sojojin Isra’ila suka kai a sansanin ƴangudun hijira na Tulkarem.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya amince da aikin soji a yankin na gaɓar yamma da tekun Jordan, sannan ya umarci jami’an tsaron ƙasar su ƙara sa ido domin daƙile wasu hare-hare a yankin.