Sojojin Isra’ila sun ce an harba kusan rokoki 70 zuwa cikin ƙasar daga Lebanon ƙasa da mintoci kaɗan.
Na’urorin tsaron sama na Isra’ila sun kakkaɓo wasu daga cikin rokokin, in ji sojojin a wata sanarwa a shafin X.
“Bayan ƙara jiniya tsakanin karfe 11:09 zuwa 11:12 na safe, an harba rokoki sama da 70 zuwa yankin Galilee daga Lebanon,” in ji sojojin.