Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Isra’ila ta amince da sharuɗɗan da za su tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki sittin a Gaza.
A sanarwar da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Mista Trump ya ce yana fatan Hamas za ta amince da wannan yarjejeniya domin, a cewarsa, lamarin ba sauƙi zai yi ba sai dai ma ya kara taɓarɓarewa.
Wakilin BBC ya ce sanarwar ta Trump na zuwa ne gabanin ganawar da zai yi da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Litinin mai zuwa, inda shugaban na Amurka ya ce zai tsaya tsayin daka kan wannan batun.
Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a baya dai ta ruguje ne a watan Maris lokacin da Isra’ila ta karya ta kuma ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza.